Politics

Me wasiƙar da El-Rufai ya rubuta wa abokansa ta ƙunsa?

Karanta rubutu kawai domin rage cin data Asalin hoton, KDGOV An wallafa Mintuna 39 da suka wuce Lokacin karatu: Minti 4 Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai, ya yi magana a karon farko a game da muhawarar da aka daɗe ana yi game da shirun da ake gani wa…

Me wasiƙar da El-Rufai ya rubuta wa abokansa ta ƙunsa?

Karanta rubutu kawai domin rage cin data Asalin hoton, KDGOV An wallafa Mintuna 39 da suka wuce Lokacin karatu: Minti 4 Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai, ya yi magana a karon farko a game da muhawarar da aka daɗe ana yi game da shirun da ake gani wasu daga cikin abokansa ko na kusa da sun yi a game da halin da yake ciki. A cikin wata wasiƙa mai taken "My Relationships and the Aftermath" wato "Abotar da na yi da abin da ya biyo baya" wadda ya sanya wa hannu a ranar 23 ga Satumba, 2026, El-Rufai ya ce wasu mutane sun nuna damuwa kan yadda wasu da ya taɓa mara wa baya a fili ko kuma yake da kusanci da su suka yi shiru a halin da yake ciki. Sai dai tsohon gwamnan bai ambaci sunayen mutanen da yake magana a game da su ba, inda ya bayyana abin da ya faru a matsayin darasin rayuwa.

El-Rufai, wanda ya shugabanci jihar Kaduna daga 2015 zuwa 2023, ya shiga hannun hukumomin Najeriya ne a watan Fabrairun 2026, bayan da hukumar EFCC ta gayyace shi domin amsa tambayoyi. A ranar 16 ga Fabrairu, 2026, ya je ofishin EFCC da kansa domin amsa gayyatar, sannan aka tsare shi bayan tambayoyin. Daga baya aka miƙa shi ga Hukumar ICPC a ranar 18 ga Fabrairu.

Lamarin ya haifar da ce-ce-ku-ce, musamman bayan sake kama El-Rufai jim kaɗan bayan EFCC ta ba shi beli a ranar 18 ga Fabrairu. Abin da ya rubuta a wasiƙar A cikin wasiƙar, El-Rufai ya waiwayi irin goyon bayan da ya ce ya taɓa bai wa mutane da dama a tsawon rayuwarsa. Ya ce a lokuta da dama ya tsaya wa mutane ko wasu abubuwa da ya yi imani da su, har ma lokacin da yin hakan ya jawo masa matsala.

"Ban yi hakan domin neman yabo ko godiya ko domin a mayar min da biki ba. Kawai na yi imanin cewa na yi abin da ya dace ne." Amma a yanzu, ya ce mutanen da ya taɓa taimaka wa su ma suna da ƴancin yin abin da zuciyarsu ta raya musu. "Wasu za su iya yin magana, wasu kuma su yi shiru.

Wasu ma za su iya musanta alaƙarmu ko kuma su yi ƙoƙarin sauya tarihin abin da ke tsakaninmu," in ji shi a wasiƙar. Daga cikin muhimman abubuwan da ke cikin wasiƙar akwai cewa tsohon gwamnan ya bayyana cewa abubuwan da suka faru a ƴan watannin nan sun sa ya sake nazarin wasu abubuwa. Ya ce: "Darasin da na koya a lokacin nan zai sa in sake nazarin yadda nake ɗaukar dangantaka da mutane duk da cewa ba sa da-na-sanin abin da na yi a baya." Ya ce ba wannan ba lokaci ba ne na zargi ko suka, inda ya ce kawai wani ɓangare ne na nazari domin fahimtar mutane da rayuwa yadda suke a fili.

El-Rufai ya kuma ce abubuwan da suka faru ba su sa ya yi nadamar taimaka wa mutane ko tsayawa da ƙarfin hali kan abubuwan da ya yi imani da su ba. Haka kuma ya ƙara da cewa ba ya jin haushin duk wanda bai tsaya masa a irin yanayin da ya taɓa tsayawa masa ba. Ya ce zai fi son ya ci gaba da kasancewa mai riƙo da halayen da suka jagoranci rayuwarsa, maimakon ya bar halayen wasu su canza nasa.

A ƙarshen wasiƙar, El-Rufai ya ce ba zai nemi ɗaukar fansa kan duk wani rashin adalci, rashin godiya ko cutarwa da aka yi masa ba. "Hukunci na ƙarshe a hannun Allah yake, kuma gare Shi ya bar wannan hukunci a duniya da lahira." Ya kuma ce kowane mutum zai rayu da zabin da ya yi, yayin da tarihi da al'umma za su samar da nasu fahimtar abin da ya faru. A ƙarshe, ya ce babban abin da ya fi damunsa shi ne ya kasance cikin kwanciyar hankali da lamirinsa da kuma Allah.

Sanarwar ta zo ne yayin da El-Rufai ke ci gaba da fuskantar shari'o'i daban-daban, ciki har da ƙarar ICPC kan zargin almundahana da kuma ƙarar DSS kan zargin kutse a wayar mai ba shugaban Najeriys shawara kan harkokin tsaro. A ɗaya daga cikin shari'o'in, kotu ta ɗage yanke hukunci kan buƙatar El-Rufai ta cewa masu zargi ba su gabatar da gamsassun hujjojin da suke zarginsa ba zuwa ranar 26 ga Oktoban 2026. Shari'o'in da yake fuskanta A ranar 24 ga Maris, ICPC ta gurfanar da El-Rufai a gaban kotun tarayya da ke Kaduna tare da Joel Adoga kan tuhume-tuhume 10 da suka shafi zargin karkatar da kuɗaɗe da sauran laifukan da suka shafi kadarorin gwamnati.

ICPC ta ce ƙarar ta shafi kusan N579.6m da dala miliyan 1.1, amma El-Rufai da abokin shari'ar nasa sun musanta zarge-zargen. Kotun ta bayar da belinsa a watan Afrilu kan naira miliyan 200, tare da wasu sharuɗɗa, bayan ya shafe lokaci a tsare. Baya ga shari'ar ICPC, El-Rufai yana fuskantar wata shari'a da DSS ta shigar kan zarginsa da yin kutse a wayar mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu.

A shari'ar, DSS ta gabatar da shaidu da kuma wani faifan bidiyo na wata hira da aka yi da El-Rufai a talabijin, inda a ciki ya yi magana kan kutsen wayar. El-Rufai ya musanta laifin da ake tuhumarsa da shi. A ranar 22 ga Satumba, 2026, kotun ta saurari muhawarar ɓangarorin biyu kan buƙatar El-Rufai na cewa masu ƙara ba su gabatar da hujjoji gamsassu ba, don haka ya buƙaci a yi watsi da ƙarar, sannan alƙali ya ɗage hukunci zuwa 26 ga Oktoban 2026.

Source: BBC

Distributed to Markets · Viral Post by RedPress.

Related News

Contact Advertise Search RSS